Rahotanni daga fadar Gwamnatin tarayya suna bayyana cewa wasu tawagar Gwamnonin Nigeria ciki har da na jam'iyyar PDP 6 zasu gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari yau Talata a Ingila
Majiyar Hausa times ta ce an shirya tafiyar ne a karkashin ofishin babban mai bawa shugaban kasar shawara a fannin tsaro, Janaral Babagana Munguno (mai murabus).
Majiyar ta cigaba da cewa an zabo Gwamnonin ne daga shiyya shida na kasarnan.
Hausa times ta ruwaito Gwamnoni 6 da ake sa ran zasu gana da Buharin sune, Udom Emmanuel (Akwa Ibom), da Dave Umahi (Ebonyi), da Abdulazeez Yari (Zamfara), da kuma Abiola Ajimobi (Oyo).
Sai dai majiyar Hausa times din tace ba'a san suwaye ragowar Gwamnoni Biyun ba.
Hausa times ta samu bayanin an bukaci Gwamnonin su kasance a filin sauka da tashin jiragen sama na Abuja sashin shugaban kasa domin tashi a yau Talata
Me zaku CE?
Source Hausa Times
Title :
Gwamnonin Jam'iyyar PDP Zasu Ziyarci Buhari Yau
Description : Rahotanni daga fadar Gwamnatin tarayya suna bayyana cewa wasu tawagar Gwamnonin Nigeria ciki har da na jam'iyyar PDP 6 zasu gana da sh...
Rating :
5