Gwamnan jihar Sakkwato yayi rashin mahaifiyansa
An yi jana'izar Hajiya Fatima Dammu a ranar Alhamis
A ranar Alhamis 6 ga watan Yuli ne gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal yayi rashin mahaifiyarsa Hajiya Fatima Dammu a garin Tambuwal dake karamar hukumar Tambuwal na jihar.
marigayiyar ta rasu ta bar yaya guda bakwai, daga ciki akwai gwamnan jihar da kuma Nura Ibrahim, Turakin Tambuwal na hukumar kwastam.
Wasu da suka halarci sallar jana’izar Hajiya Fatima sun hada da gwamnan Tambuwal, Mataimakin gwamna Ahmad Aliyu, Sakataren gwamnati Farfesa Bashir, kwamishinoni da sauran masu fada a ji a jihar.