Rahotanni daga jihar Bauchi sun bayyana cewa Gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar ya sanar da sauke duka kwamishinoninsa daga mukamansu a yau Alhamis.
A wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Shamsudden Abubakar ya fitar dauke da sa hannun babban sakataren na sha'anin siyasa da al'amuran yau da kullum na jihar, Sa'idu Abubakar Maikobi yace Gwamnan ya kuma sauke sakataren Gwamnatin jihar, Bello Shehu Ilelah
Saidai Gwamnan bai bayyana dalilin yin garambawul din ba. Amma dai ya godewa daukacin kwamishinonin bisa goyon bayan da suka nuna masa da kuma sadaukarwar da sukayi na yiwa jihar aiki a karkashinsa
Title :
Gwamnan Bauchi Ya Sauke kwamishinoninsa Da Sakataren Gwamnatin jihar
Description : Rahotanni daga jihar Bauchi sun bayyana cewa Gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar ya sanar da sauke duka kwamishinoninsa daga ...
Rating :
5