Daga Kwamared Zakari Y Adamu Kontagora
Wani matashi mai suna Hassan ya rasa 'yan yatsun sa sanadiyyar saran da wani bafullace mai suna Garba yayi masa, lamarin yafarune a yau Juma'a a garin Matane dake karamar hukumar Mashegu ta Jihar Neja.
Wani mazaunin garin Mashegu mai suna Malam Nura Alhassan Jigawa da ya shaida al'amarin ya shaida wa wakilin mu cewar " al'amarin ya faru ne a lokacin da Bafullacen ya shigo cikin garin ya sayi taba sigari ya kunna yana sha a cikin al'umma, sai matashin ya ce masa dan Allah ya koma gefe har ya kammala shan sigarin domin ba ya son warin sigari, a cikin fushi sai Bafullacen ya ce masa karda ya raina masa wayau, daga nan takaddama ta kaure tsakanin su ana cikin hakan sai bafullacen ya zaro adda ya kaiwa matashin sara ganin haka sai matashin ya tarba hannu dan ya kare sanadiyyar hakan ya sare masa yatsun hannu.
'Yan uwan matashin na ganin hakan sai sukayo ca kan bafullacen inda suka haushi da duka, amma jami'an tsaro na 'yan sanda sunyi nasarar kwatansa hannun matasan, yayin da aka garzaya da matashin asibitin garin Mashegu domin yi masa aiki.
Al'amarin da ya fusata 'yan uwan matashin inda suka yi yunkurin kai farmaki na ramuwar gaiya ga 'yan uwan bafullacen, sai dai jami'an tsaro da dattijan garin na Matane sun yi nasarar shawo kan matasan, yayin da zaman lafiya ke cigaba da wanzu a cikin garin da kewaye.
Title :
Graphic Photos: Wani Bafullace Ya Sare Wa Wani Matashi Yatsun Hannu A Jihar Neja
Description : Daga Kwamared Zakari Y Adamu Kontagora Wani matashi mai suna Hassan ya rasa 'yan yatsun sa sanadiyyar saran da wani bafullace mai suna...
Rating :
5