Masu sana'ar karuwanci a Nigeria sun nemi Gwamnati ta halasta sana'ar karuwanci a kasar, sannan a daina nuna tsangwama ga masu yin sana'ar
Kiran hakan ya fito ne daga shugabar kungiyar mata karuwai ta Nigeria, Amaka Anemo,
Amaka tace halasta jima'i a matsayi sana'a zai rage yaduwar cutar sida sannan zai bayar da kariya ga masu yin sana'ar
Shugabar matar tace so tari jami'an doka idan suka kama su suna karbar kudade ne hannunsu a yayinda lokuta da dama kuma suke kwana dasu a matsayin fansa. Tace galibi kuma jami'an dokar basa amfani da kariya wanda hakan ka'iya zama hadari
Hausa times ta ruwaito Amaka na fadin, akwai fitattun mutane masu nuna kyamar sana'ar a bayyane amma kuma suna so a boye, kuma mafi yawa sune manyan kwastomomi.
Tace a irin haka sai miji ya lallaba ya je ya kwaso cuta yaje ya shafawa iyalinsa ko budurwarsa wacce itama zaka samu tana da nata saurayin a boye itama ta goga masa. Tace amma idan aka halasta sana'ar karuwan zasu fi jin dadi wajen tsaftace sana'ar tasu da inganta ta kuma zasu fi samu a kula da kiwon lafiyarsu
Shin kun goyi baya a halasta sana'ar karuwanci a Nigeria?
Daga Hausa Times
Title :
Gamayyar Mata Nason A Halasta Sana'ar Karuwanci A Nigeria
Description : Masu sana'ar karuwanci a Nigeria sun nemi Gwamnati ta halasta sana'ar karuwanci a kasar, sannan a daina nuna tsangwama ga masu yin ...
Rating :
5