Kungiyar Fulani ta GanAllah da ke Najeriya ta shirya shigar da kara a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC da ke Hague, mako mai zuwa.
Kungiyar ta Fulani dai ta yi zargin cewa an yi wa al'ummar Fulanin kisan kiyashi a Mambila da ke karamar hukumar Sardauna a jihar Taraba. A 'yan makonnin da suka gabata ne dai aka yi ta samun rikici mai nasaba da kabilanci tsakanin Fulani da Mambilawa.
Alkaluman da ba na gwamnati ba sun nuna mutane kimanin dubu daya sun mutu sannan an kashe dabbobi fiye da dubu uku. Kungiyar ta GanAllah ta ce tana zargin gwamnatin jihar da hannu a cikin rikicin.
Title :
Fulani Makiyaya Za Su Maka Gwamnatin Taraba Kotun Duniya
Description : Kungiyar Fulani ta GanAllah da ke Najeriya ta shirya shigar da kara a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC da ke Hague, ma...
Rating :
5