Gwamnan Jihar Ekiti, Mr. Ayodele Fayose, ya yi barazanar zai saki wasu hotuna guda goma sha daya wadanda za su tabbatar wa 'yan Nijeriya cewa lallai rashin lafiyar Shugaba Muhammadu Buhari ya tsananta sabanin yadda ake ta rade-radin ya samu sauki.
A cewar Fayose, babu gaskiya ko kadan a zancen mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo inda ya bayyana cewa Shugaba Buhari na murmurewa yadda ya kamata biyo bayan ziyarar da ya kai wa Shugaba Buharin kwanan a can birnin Landan inda yake jinya.
Gwamnan dai ya yi wadanna kalaman ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai jiya Laraba a birnin tarayya, Abuja, tare da cewa abin da ya fi dacewa shi ne, Shugaba Buhari ya yi murabus ya ajiye aiki sannan ya fuskanci ceto lafiyarsa.
Daga Rariya
Title :
Fayose Ya Yi Barazanar Fallasa Halin Rashin Lafiyar Buhari
Description : Gwamnan Jihar Ekiti, Mr. Ayodele Fayose, ya yi barazanar zai saki wasu hotuna guda goma sha daya wadanda za su tabbatar wa 'yan Nijeriy...
Rating :
5