Sabuwa duk abin duniya ya isheta saboda yadda Zulai ta rinka yi mata fada. Tana kwance kan katifarta zuciyarta tana mata saka da warwara. Inuwa ne ya shigo dakin ya nemi kwanciya kusa da ita. Wani tsami ne ya daki hancinta ta mike cikin fada. Don wulakanci banda rashin abinci a gidanka kullum sai ka kwanta min kana wari? Don Allah ni ka tashi jiki sai tsami kamar kayi wanka da kwata. Ya tashi ya kai mata duka ta rike hannun sannan ta kwada masa wani kwantareren takalmi a ka. Cikin karaji ya biyota waje suna ta fada sai ta tuna hudubar zulai. Nan da nan ta fara zaginsa tana cewa ya saketa sanin cewa yana da saurin fushi. In sake ki ko Sabuwa? Ni kike cewa na sake ki ko? Ta eh in dai ka haifu cikin uwa da uba. Ransa ya kara baci har kin manta sakin da nayi miki kwanaki Zulai ta rinka hadani da Allah na mayar dake ko? Ai da kenan Inuwa yanzu kuwa na gaji bazan zauna yunwa ta kashe min 'ya'ya ba. Yayi dariya makota duk sun saba jinsu kije Sabuwa na sake ki saki daya amma wannan karon kada kuzo biko don wata zan nema. Kuma ki tafi ke kadai don a nan kika sami yaran ba dasu kika zo ba. Ita kalmar sakin kawai taji tasa kuka wallahi inuwa wasa nake don girman Allah ka mayar dani kafin kowa ma yaji. A zuciyarta fatan ta daya ya mayar da ita. Ina zata idan ta bar gidansa? Gwaggonta da kyar take ciyar da kanta gashi sauran yayyenta duk sunyi aure. Me ya kaita ma yarda da shawarar gwaggo. A wurin girki ta kwana washegari yayo fatali da ita da kayanta.
Cikin kuka ta karasa gida. Gwaggo Zulai na ganinta da kaya da kumburarriyar fuska ta tashi cikin sauri. Ya sake ki ko Sabuwa? Ai dadina dake jin magana. Sabuwa ta turo baki ta zauna kan tabarma yanzu Gwaggo baki damu da dukan dana sha ba sai saki ko. To ya sakeni amma wallahi idan baki yi min tanadi mai kyau ba sai na jawo miki magana a unguwar nan. Zulai ta rike baki lallai yar nan baki da kunya. To ki kwantar da hankalinki Yakubu zan tabbatar kin aura.
Tani duk ta zayyanawa iyayen su abinda Uwale tayi wa Munari. Babar su Tani Inno tace to ai inda sabo ta saba sai tayi hakuri. Shi kuma yaron Allah Ya jikan shi. Inna Ladi kishiyarta babar su Salihu tace Allah Ya shiryeki Jummai. A fada miki abinda tayiwa auta shine zaki wani tabe baki. Allah Ya jikan Malam amma da yana nan bazai lamunci wannan abin ba. Bari Yayan ku ya dawo daga birni Tani da kanshi zashi gidan. Inno tace haba Yaya don Allah kada ma ya sani. Yanzu sai kiji yana cewa a sako masa kanwarsa. Inna Ladi tace to tashi muje gidan. Inno tace ni ba zani ba Yaya rigima ce bana so. Inna Ladi ta sabi mayafi suka fita ita da Tani bayan ta ajiye yaran wurin Inno.
Batul Mamman
Title :
FARAR HAIHUWA💰4
Description : Sabuwa duk abin duniya ya isheta saboda yadda Zulai ta rinka yi mata fada. Tana kwance kan katifarta zuciyarta tana mata saka da warwar...
Rating :
5