Salati da ihun mata yasa su Munari fitowa daga daki. Mata na ganinta suka yi cirko cirko an rasa mai magana tana ta tambayar me ya faru. Uwale tace ni dai ba ruwana ,fa bani bace. Munari tace wai meye ne? Me kuke leqe a rijiyar? Wata makociyarsu ce tayi karfin halin fada mata...Ramlah ce ta fada.
Wata kururuwa Munari tayi cikin zafin nama ta nufi rijiyar ana rirriketa. Tani tace cikin rudewa garin yaya ta fada? Wata yar cin shinkafar sunan tace qashi ne Hanne ta jefa mata bakin rijiya shine ta bishi ta fada. Mal Yakubu aka fita kira a majalisarsu. Munari tun tana kuka da sauti har muryarta ta dashe....wayyo Allah kawai take cewa. Abin tausayi ta zama.
Mal Yakubu ya shigo yana tambayar me ya faru ake nemansa. Munari ta mike ta rije wuyan rigarsa. Baban Ramlah idan na rasa 'yata bazan zauna a gidan nan ba. Yi hakuri ki fada min abinda ya faru. Wani yaro yana cin nama yace 'yarta ce ta fada rijiya. Mal Yakubu yace Ramlah? Babbar riga ya tube zai shiga shima aka rike shi. Uwale ta soma kuka don Allah dan nan kada ka shiga kaima ka mutu. Suna haka Sabi mai hakar rijiya ya shigo da wasu maza. Igiya mai kauri aka daura masa ya shiga. Duk sakan a wurin su Munari tamkar shekara suke jinsa. Kamar wata zautacciya haka ta koma. Sai bayan kusan minyi goma ya fara jan igiyar. Cikin sauri aka jawo shi da Ramlah a kafadarsa. Mal Yakubu ya karbe ta ya kwantar akan tabarka. Cikinta ya danna ruwa y rinka fita ta bakinta da hanci. Munari ko wurin bata je ba tana zaune inda wasu mata suka riketa ta share hawaye Allah Ya jikanki Ramlah kawai take fada.
Duk yayi iya yinsa ya tabbatar yarsa ta rasu. Cikin kuka ya bude hannun da yaga ta damke sosai. Qashin data dauka ne ashe ba rabonta bane. Wace 'yar....din ce ta jefa kashin bakin rijiya? Jin kowa yayi tsit ya sake kunduma zagi cikin tsawa. Aka samu wata ta nuna Hanne. Kanta yayi kamar zaki cikin fushi wani abokinsa ya rike shi. A tsorace tace Uwale ce tace min mayya ce na jefa mata qashi shine tautsayi yasa na jefa bakin rijiya. Suna wannan fadan Munari ta dauke gawar yarta ta kai daki ta fara shirin yi mata sutura. Taron suna ya koma na mutuwa ita dai Uwale tayi tsit don yau dan nata ya bata tsoro. Yana matukar son Ramlah sosai. Bayan an tafi kaita ne Munari tana zaune gaban iyayenta da suka zo ta fara jan numfashi da kyar. Mal Yakubu aka kira ya zo ya fitar da ita a rude. Ya kalli innarsa cikin bacin rai. Idan itama ta mutu yau zan saki Sabuwa kuma ta tafi da yarta bana so. Asibiti suka nufa inda likita ya tabbatar jininta yayi mugun hawa kuma tana dauke da ciki na wata daya. Duk da bakin cikin dake damunsa Mal Yakubu yayi matukar murna. Ta taga yake leken matarsa saboda ance a barta ta huta sosai. Yana adduar ta sami lafiya.
Bayan kwana takwas da rasuwar Ramlah Inna Ladi tazo gidan da sauran yaransu mata hada kayan Munari. Mal Yakubu yana ta bada hakuri yana zubar da hawaye. Inna Ladi tace kaga ka bari mu tafi ta laluma kafin yayanta ya zo kaima tunda baka ganshi ba kasan baya gari ne. Kiyi hakuri inna ya zan saki Maimuna a wannan lokacin ga rashin 'ya ga kuma rabo a tare da ita. Inna Ladi ta kalle ta Munari da gaske ne? Kanta ta sunkuyar kasa sai hawaye. Yi shiru kinji kada ciwonki ya tashi. Ta dubi Uwale dake zaune tana yiwa Hannan rawa Sabuwa tana bacci a daki. Yakubu kasan kashe min jika akayi da gangan muka hakura yanzu haka zata zauna cikin bakin cikin rayuwa a gidanka? Kiyi hakuri inna babu fa wani yanayi mai dorewa. Zan kula da ita muddin raina bazan bari wani ya wulakanta ta ba,yana magana yana kallon Inna Uwale. Ta dago kai nasan dani kake dan nan ka cigaba da zargina don kawai yarka ta mutu. Ba ga wata Allah Ya baka ba? Girgiza kai yayi ya cigaba da bawa su Inna hakuri.
Tun daga lokacin babu me shiga harkar Munari a gidan saboda yadda iyayenta suka sa musu ido. Sai habaici daga gefe. Mijinta kuma yana nuna mata so da kulawa sosai suna ta rainon cikinta cikin sirri. Wata rana suna cin abinci tace ni kuwa Mal meyasa baka so su inna su san ina da ciki? Munari kenan ai ba murna zasu yi ba. Karshenta a rinka yin abinda zaa bata miki rai har ciwonki ya tashi. Ko kin manta Yaya Salihu yace duk ranar da jininki ya hau ko zanyi kukan jini sai na sakeki. Dariya tayi masa aikuwa gobe zanyi masa aike. Au tsokanata ma kike ko? Zan rama ne... yanzu dai kiyi ta sa hijab da zaman daki so nake kawai Inna taji haihuwa. Allah ba don darajar ta haifeni ba da tuni nasa an daure....hannu tasa ta rufe masa baki. Haba Mal? Ka manta Allah Yace kada mu fadi kalma mara dadi game da iyayenmu? Kada ka manta kwananta ne ya kare mu kuma hakurinmu shine ladanmu. Hakane Munari nima yau na dana. Allah Yayi miki albarka Ya saukeki lafiya. Amin M[truncated by WhatsApp]
Title :
FARAR HAIHUWA PART 8
Description : Salati da ihun mata yasa su Munari fitowa daga daki. Mata na ganinta suka yi cirko cirko an rasa mai magana tana ta tambayar me ya faru...
Rating :
5