Sabuwa ta ware idanu kai Gwaggo ai kinga auren babu iddah ma ba kyau ko? Zulai ta banza rufe min baki. Inji uban wa aka ce ba kyau. Aure kan aure ne ba kyau kuma dai ba shi zakiyi ba tunda ya sake ki. To cikin fa? Shi ciki ai ba matsala kinsan Uwale babu abinda ba zatayi ba akan farin jika. To nasan tana da gonaki biyu na gadonta kinga ko ita muka samu mun huta. Sabuwa dai bata gamsu ba tace Gwaggo zunubin fa. Ai dan zai zama shege...kul kika kira shi shege da ubansa fa. Ina fata bai san da cikin ba? Eh bai sani ba. Zunubin kuma zamuyi ta cewa astangafirillah sai kiga Allah Ya yafe. Sabuwa tace Astagfirullah dai Gwaggo. To naji yanzu dai kin amince ko. Na amince Gwaggo. Sukq zauna suka kulla duk yadda zasuyi a gidan Uwale idan aure ya yiwu. Saar su daya kauyen da Sabuwa ke aure daban da nasu saboda haka da wuya yaji labarin auren.
Shirye shirye ya kankama na bikin Sabuwa da Mal Yakubu. Uwale da Zulai le kidansu da rawarsu don shi angon ko a ransa. Kullum yana rarrashin Munari ta kara hakuri idan ya sami kudi zai raba musu gida da Inna Uwale. Ana saura kwana biyu Yaya Salihu yazo garin Danmarka gaida iyayensa shi da matarsa Ruma. Tani na jin labarinsa ta tafi gidan ta zayyana masa halin da Munari ke ciki. Fada ya rinka yi iyakar karfinsa Inno tana bashi hakuri. Inna Ladi tace ni bazaka burge ni ba sai kaje gidan kayiwa uwarsa barazana yadda zata yi shayin takurawa 'yata. Kamar jira yake ya tafi gidan cikin fushi. A bakin kofa ya gamu da Mal Yakubu ya fara zazzaga masifa. Mal Yakubu duk ya tsorata yana ta bashi hakuri. Har gidan ya shiga sukayi ta da Uwale yace ke Maimuna dauko mayafinki ya kama hannun yaran..birni zamu tafi kai kuma ka biyoni da takardarta. Mal Yakubu dai harda kuka itama Munari tana yi. Da kyar Yaya Salihu ya aminci ya barta amma ya dauke Sadi dashi zan tafi. Mal Yakubu yace wallahi na bar maka shi don girman Allah kada ka rabani da matata. Yaya Salihu yace mata zan kaiwa Ruma kinji ko munari sai ta hada shi da Ali su shiga makaranta idan sun dan kara girma. Godiya tayi masa ya kawo kudi ya bata. A waje ya sake jaddadawa Mal Yakubu ya kular masa da kanwa sannan idan anyi auren zai sa ido a kansa. Daidai da rana daya yaji zance mara dadi zai dauki mataki.
Ranar lahadi da karfe biyun rana bayan an idar da sallar azahar aka daura auren Mal Yakubu da Sabuwa. Dakinsa aka saka amarya ya zama bashi da daki a gidan sai na wadda take da girki. Da daurin gindin uwale Sabuwa ta goge da yiwa Munari wulakanci a gidan. Kullum hakuri take saboda yadda mijinta ke iyakar kokarinsa wurin kyautata mata. Watan Sabuwa biyu a gidan ta fara bayyana cikinta kamar yadda suka yi da Zulai. Uwale kamar ta lashe ta don so. Kullum Zulai tana gidan abinci safe ,rana da dare duk an mata kwano. Habaici iri iri Munari take sha idan suka hade kansu karkashin bishiya da yamma. Kirikiri Uwale ta hana Sabuwa girki kullum Munari keyi idan dare yayi kuma ta tubure tace sai Mal Yakubu ya shigo dakinta ranar girkinta.
Batul Mamman
Title :
FARAR HAIHUWA PART 6
Description : Sabuwa ta ware idanu kai Gwaggo ai kinga auren babu iddah ma ba kyau ko? Zulai ta banza rufe min baki. Inji uban wa aka ce ba kyau. Aur...
Rating :
5