A tsakar gida suka tarar da Munari tana iza wuta ga hayaki saboda yanayin damina icen duk ya jike. Inna Ladi tayi saurin zuwa wurin ta karba. Da kyar Munari ta iya durkusawa ta gaisheta. Inna Ladi tace haba mike...ina kike Uwale fito Allah Ya tona asirin ki. Yanzu yar ta haihu jiya, haihuwar ma mai ciwo tunda ba dan amma don tsabar wulakanci da kanta zata dora ruwan wanka da wannan icen haka? Uwale ta cangalo kafa daga daki ta fito. Idan kun damu da ita sai ku dora mata. Inna ladi tace tafiya muka yi jaje gidan kanin babanta garin kwari shiyasa tani bata same mu a gida ba . Dama tace jiyan ma ita ta dora ruwan. Haba Uwale rashin imanin naki har ya kai nan. Uwale tayi wani juyi ita ga mai kyau...ta tafa hannuwa yafi nan Ladi. Ki tambayeta abinda tayi min. Dan farin ne fa ya mutu sai wadan can gawayin kullum su nake gani a gidan nan. Sannan ace bazanyi fada ba. Inna Ladi tace Munari dauko gyalenki wallahi na gaji da wannan diban albarka. Idan yayanki ya dawo sai ayita ra kare. Tana gama magana Mal Yakubu ya shigo da dan guntun ragonsa kafi zuru. Jin abinda ake fada ya karasa gaban matarsa. Munari don Allah kada ki tafi. Inna Ladi ki rufa min asiri kada ku raba ni da ita. Hawaye ne taf a cikin idonsa Uwale na gani tace kwarankwatsa ka bari hawayen nan suka fito gaban surukarka sai na daga maka nono. Da kaji anyi zancen saki sai kuka kamar ka auri hurul...hurul me ma? .oho matan aljannah dai nake. To ka zabi daya ko ka sake tan ko kuma nan da sati biyu ka auri duk wadda na zaba maka. Da hanzari yace zanyi auren inna. Ya koma kallon Munari koma daki in dafa miki ruwan kinji. Kinga rago can na siyo zan gasa miki. Sosai Inna Ladi taji tausayinsa amma sai ta dake ni dai tafiya zanyi da ita mun gaji. Uwale tayi tsaki aikin banza kin saki baki kishiyar uwa zata kashe miki aure kin zata sonki take. Makirci ne kawai irin namu na mata. Munari sai a lokacin tayi magana.. Inna ki dena fadin abinda kika ga dama kan Innarmu don akanta wallahi zan....zaki me??? Kaji ko dan nan matarka zata zageni. Inna Ladi tace Tani dora ruwan wankan ko sake kallon Uwale bata yi ba taja hannun Munari suka koma daki.
Bayan kwana hudu da haihuwar munari Uwale na zaune karkashin bishiya tana shan fura Zulai ta shigo. Tana ganin furar yawunta ya tsinke. Ita kuwa uwale bata san tana yi ba kuma bata yi mata tayi ba. Can ta lura da kallon da Ramlah ke yi mata. Ta ja tsaki shegiya mayya duk ta kafa min ido zo ki karba. Yarinya ta taso daga wurin wasanta tazo gaban uwale. Dan yatsa ta tsoma cikin furar ta dangwala mata a harshe. Ramlah ta lashe tas ta koma wasa. Zulai dai abin duniya ya isheta sai ta fara tunanin abubuwan tausayi da suka sameta kamar rashin abinci da rashin tayin fura daga kawarta. Nan da nan sai ga hawaye Uwale ta tande baki tace lafiya zulai. Uhmm ina fa lafiya Uwale. Ina ta faman nema miki yarinyar da Yakubu zai aura jiya da daddare sai ga Sabuwa. Uwale tace fara gaya min zancen yarinyar kafin muyi zancen sabuwan. Zulai ta sha kunu Uwale baki da kara fa. Aurenta fa ya mutu. Ajiye ludayin tayi eyye kika ce me? Nace aurenta ya mutu. Ashe wata biyar kenan da mijin ua saketa bata fada ba ta zauna gidan tana son ya mayar da ita gashi har iddah ta kare. Jiya yayi mata korar kare. Sai wasu hawayen ke zubuwa daga idon Zulai ganin kudaje na bin kokon furar tasan sarai uwale na gani zata zubar da ita gaba daya. Uwale tace to ai ki bar binciken haka tunda har ta gama iddah kuma na tuna duk yaranta farare ne. Ki bar komai a hannuna ranar asabar zata tare a gidan wannan alqawari ne. Zulai sai murna , uwale tace ga fura ki sha. Kafin ta rufe baki Zulai ta janye kokon ta kafa kai. Mayunwaciya Uwale ta fada a sarari.
Tana zuwa gida ta sanar da Sabuwa yadda suka yi. Ni dai na fada musu kin gama iddah idan ba haka nayi ba kinsan uwale da rashin hakuri kamar zawo sai ta bashi wata. Sabuwa ta hadiyi yawo da kyar tace Gwaggo ina jin ciki gareni fa wata kusan biyu. Muhuci zulai ta kwala mata a ka. Baki da aiki sai ciki ne duk yunwar gidan inuwa. To bari kiji. Ranar asabar zaa daura aurenku sai kiyi shiru da bakinki. Idan kika haihu sai muce bakwaini[truncated by WhatsApp]
Title :
FARAR HAIHUWA PART 5
Description : A tsakar gida suka tarar da Munari tana iza wuta ga hayaki saboda yanayin damina icen duk ya jike. Inna Ladi tayi saurin zuwa wurin ta ...
Rating :
5