Mal Yakubu ya fito da dan kudi daga aljihunsa ya nuna mata. Kinga na ajiye saboda siyan rago amma tunda haka Allah Ya qaddara mana sai ki fada min abinda kike so na saya miki. Tasan duk don ya kwantar mata da hankali ne saboda abinda inna Uwale tayi mata. Tace haba baban Ramlah ka bari muje gida mana. Ya girgiza kai kinsan Allah maimunatu bana son Yaya Salihu yaji zancen nan. Kinga lokacin haihuwar Sadi da inna ta hana a yanka masa rago cewa yayi na sake ki ba dole bane auren. Maimunatu bazan iya rayuwa da wata mace ba bayan ki. Don girman Allah kada ki bari a raba mu. Murmushi tayi bata manta yadda ya rinka rokon yayanta ba har saida iyaye suka shiga maganar. Tace ni da kai Malam Yakubu mutu ka raba. Dariya yayi sosai sannan ya fita neman taxi da zata kai su gida.
A tsakar gida Inna uwale da zulai suka zauna tana ta bambami tun a hanya. Ni munari zata cuta? Ni uwale wallahi sai anyi min farar haihuwa a gidan nan. Sai naga jika mai kyau da daukar hankali zulai, sai jikana mace ko namiji yayi kudi. Ni banda abin namiji ma ina tsiya ina bakar fata. Munari fa banda hakora ni ban taba ganin wani abu mai haske a jikinta ba. Zulai dai sai bada baki take don tana samu a wurin aminiyar tata. Bayan sunci abinci Uwale tace ke ni a ina zaki samo min farar mace bazawara mai 'ya'ya ne.? Zulai ta ware ido farar bazawara mai 'ya'ya fa kika ce uwale. Eh saboda su hadu da dannan su haifi farare. Ko wacce iri ce indai fara ce ina so. Don ma duka yaranki sunyi aure ne ai da ko Sabuwa ya aura dama ita naso masa tuntuni. Zulai tace to zan duba Uwale gashi kinga Sabuwan ma suna ta fada da mijin gashi haihuwarta biyu. Dan karen kwadayi gare da zulai duk talaucin gidan Uwale sun fita arziki nesa ba kusa ba ga rashin abinci. Uwale tace ki barta a gidanta a samo wata saboda idan an kashe auren sai tayi idda fa. Ni kuwa so nake nan da sati biyu ma amarya ta tare. Zulai tace to bari na tafi kinsan da zafi zafi ake dukan karfe.
Gidan Sabuwa ta nufa ta tarar da ita da mijin suna fada saboda babu abinci a gidan ga yaranta suna jin yunwa. Zulai ta zakalkale kamar ba suruka ba yana ta basu hakuri suna zaginsa. Karshe zulai tace kaga Inuwa ka sakar min 'yata yanzu wallahi ko in hadaka da 'yan sanda. Yaro mara kunya haka ko yau ka saketa zata sami mijin aure. Ai farar mace kadara ce. Idan kaki kuma wallahi sharri zan kulla maka wanda zaisa ka raina kanka. Yace haba Gwaggo meyayi zafi haka? Ni bazan saketa ba. Sabuwa tace Gwaggo ban fa gaji da auren ba kawai don babu abinci sai kice ya sake ni. Ta zumburo baki. Zulai ta make bakin banza zan miki gata kina min fitsara. Zulai ta ja hannunta suka shiga daki ta fada mata hadin da take son yi. Kinga idan kika haifi farin da uwale ke jarabar so wallahi sai yadda muka yi da ita. Kina kallo dai yadda kike wahala nan ga fararen 'ya'yan shegen mijinki baya gani. Sabuwa ta bata rai Gwaggo nifa ina son sa gaskiya. zulai ta saki wata ashariya Sabuwa zan miki rashin mutumci fa. Bar ganin ni na haifeki bani da kyau a harkar samu. Ki tada balli a daren yau ya sallameki kawai.
Batul Mamman
Title :
FARAR HAIHUWA Part 3
Description : Mal Yakubu ya fito da dan kudi daga aljihunsa ya nuna mata. Kinga na ajiye saboda siyan rago amma tunda haka Allah Ya qaddara mana ...
Rating :
5