Da dafa bango Munari ta fito daga dakin nurse na biye da ita da jaririn. Tani ta gyara goyonta ta mika hannu zata karbi dan Uwale tayi saurin shigewa gabanta tace bani nan. Ni na haifi ubansa. Tana bude zani ta kwala ihu ta mikawa zulai dan ta kai goshinta kasa tayi sujjada. Allah nagode maka...ta kalli surukarta munari kin kwaci kanki wallahi. Ke dai Allah Yayi miki albarka. Da kanta ta rike Munari suka karasa dakin aka bata gado. Tani da mijinta suna ta yi mata sannu. Inna uwale ta sake karbar dan tana ta washe baki tace jamaa kunga abin arziki ko. Yarinya mai son gamawa da duniya lafiya kenan. Ashe tumatir da su mangwaron dana rinka siya miki yau kinga ranarsu ko. Ashe banyi asarar kudina ba. Zulai ai na fada miki duk miyar kadi ko harkar daddawa sai da na hanata gashi kuwa kwalliya ta biya kudin sabulu. Kiri kiri ta hana kowa daukarsa saboda tsabar murna. Zaninta taji zai kwance ta mikawa Zulai dan ba don taso ba tana magana. Ai sunan babana zaa saka maka yaro. Nima a nan na gado farin da kyau har kaima ka dandala. Zulai ta dan jujjuya yaron a firgice Uwale tace ya haka ne? So kike ya fadi? Zulai tace a'a fa Uwale gani nayi kamar baya motsi. Kinga fa ko kuka baiyi ba. Allah tsine mai karya ta fada tare da karbe dan. Ai kuwa abinda zulai ta fada gaskiya ne. Uwale ta juya shi shiru ba motsi. Yaro ga shi fari kato ga kyau amma bai zo da rai ba. Da cangala kafar uwale ta fita kiran nurse kuzo ku daba min dannan na shiga uku na ni Hadiza ina zan sa kaina. Nurse tazo tace a'a maimunatu baki fada musu yaron bashi da rai bane? Hawaye ne ya sauko mata tace yanzu zan fada. Tani ta zauna gefen gadon ta rungumeta. Yi hakuri Munari Allah Yasa mai ceton mu ne Ya yi masa rahma. Mal Yakubu ya ajiye Sadi ya karbe yaron daga hannun Uwale ya kare masa kallo sannan ya rufe shi sosai da zanin. Uwale cikin kuka tace yanzu mai kyan ne ya mutu? To wallahi kasa a ranka Yakubu kamar kayi aure ka gama. Kan uba ni zaki yiwa haka munari? Ki haifi bakake digirgir farin kuma ya koma. Yar purse dinta ta dauka tace Zulai zo mu tafi gida. Daga bakin kofa tace tsakanin na dake munari Allah Ya isa, muguwa mai bakar aniya.
Suna fita Tani tace gaskiya baban Ramlah abinda Inna tayiwa Munari bata kyauta ba. Wannan wane irin rashin imani ne. Mace ta rasa danta a rinka binta da bakaken maganganu. Wallahi sai na fadawa Yaya Salihu ai ba daga sama ta fado ba tana da dangi. Munari tace Yaya Tani kiyi hakuri don Allah. Ya zaki bani hakuri bayan ke aka batawa Munari... mal Yakubu ya rinka bata hakuri. Yaya Salihu mutumin kirki ne amma akan yan uwansa bashi da kyau duk da kasancewar ba uwa daya suke ba amma iyayensu na zaman lafiya. Jafaru ta kira danta mai kimanin shekaru takwas. Yana shigowa yace Umma Munari sannu. Ta dan murmushi yauwa dan albarka. Tani ta goya masa Sadi ta rike hannun Ramlah. Bari mu tafi munari yaran nan basu ci abinci ba na taho dasu. Mal Yakubu ya kara bata hakuri. Yanzu zamu taho muma zan nemo dan tasi ne saboda jikinta.
Batul Mamman