FARAR HAIHUWA1
Bismillahir Rahmanir Rahim
Kai kawo take tayi a siririn corridor din asibitin cikin tsananin tashin hankalin rashin sanin halin da kanwarta take ciki. Inna Uwale dake zaune a kan tabarma ta daga hannu sama idanunta duk sun ciko da hawaye tace Ya Allah ka bani farin jika ko wanne iri ne. Ya Allah fari kyakkyawa kamar ni. Zulai aminiyarta tace amin amin Uwale ai ranar sai munyi sadaka. Tani dake kai kawo da sauran matan da 'yan uwansu ke cikin dakin haihuwar suka zuba mata ido. Ta kuwa cigaba da adduar farin jika kamar yadda ta saba. Cikin kunar rai Tani tace amma Uwale baki da mutumci ko kadan. Kanwar tawa tana ciki rai a hannun Allah kina wani fatan a haifa miki farin jika. Farin jikan yaci.....bullowar mal Yakubu yasa tayi shiru ta share hawayen bakin cikin da ke shirin sauko mata. Ita kuwa Inna Uwale tace ashe baki da kunya Tani? Ban girmi uwarki Baraatu ba? Ita dai Tani shiru tayi don tana gani mutumcin Mal Yakubu mijin kanwarta. Yayi gumi sharkaf saboda tafiyar da yayi zuwa asibitin a kafa bayan dan Tani din ya bishi gona ya sanar dashi halin da ake ciki. Ramlah da Sadi suna ganinsa suka mike suna murna suka tsaya a gabansa. Daukar Sadi yayi itama Ramlah tasa kuka sai an dauketa. Tana kukan bata sani ba ta taka kafar Inna Uwale. Wata kara ta saki kafin ta hankade ta ta fadi kasa. Matsa can gun yar uwarki, shegiya baka mummuna. Mal Yakubu yace haba inna a nan din ma. Tani ta dauke ta tana goge mata bakinta da yasha kasa. Yarinya sai kuka take. Yo ba kaine duk ka cuceni ba dan nan. Mata aka sami abin kallo jin yadda Uwale ta bude murya. Ta cigaba dube ni nan ga fari ga kyau haka Allah Yayi ni tun kuruciya don ma girma yazo. Ta daga siririyar kafarta ta hagu wadda shan inna ya shanye tace da wannan Allah Ya ragewa aya zakinta duk kyan dire na ban sami mijin arziki ba sai ubanka. Allah dai Ya jikansa. Babu irin adduar da banyi ba da cikin ka don ka fini sanin baki ne. Allah Ya taimake ni na haifo ka fari tas ga kyau. Sai hawaye shar suka sauko mata ya durkusa kasa don Allah Inna kiyi shiru. Sauran matan dake wurin suna ta kallo an sami labarin kaiwa gida yau. Yaron nan da yake mai bakin kashi ne ya rasa wadda zai aura sai yar maiduguri. Wallahi kunga wannan yayar tata ta nuna Tani har ta fita haske. Kalarta fa kamar dauda yadda dai kuka ga 'ya'yan nan. Ba yadda banyi ba har da kwanciya a asibiti duk don a fasa auren yaki jin maganata. Ga haihuwar balai duk shekara. Yanzu wannan cakurkurar, ta nuna Ramlah zaayiwa kani na biyu. To ni mijina ba arziki har ya mutu shima dan babu. Ni kuwa kafin na mutu sai naje makka da kudin jika ko na mijin jika. Haka kawai yadda nake da kyan nan bazan bar baya bakikkirin ba. Mal Yakubu ya share hawayen idanunsa. Inda sabo ya saba da halin innarsa amma irin wannan a cikin mutane ta gama zubar masa da mutumci.
Goron bakinta ta furzar tace wallahi indai ta haifi fari ko fara nayi alqawarin yi mata wankan jego da hannuna. Ga mutane suna min shaida. Ni ban tsani Munari ba harkar bakar fata ahalin tsiya da talauci ne bana so. Tana gama magana wata nurse ta fito tace ina wadanda suka kawo Maimunatu Ado? Mal Yakubu yayi saurin matsowa gaba. Inna uwale ma ta cangalo kafa tace Nas fada min me aka samu. Fari ne? Ko kallonta nurse din bata yi ba tace masa ta sauka lafiya za'a fito da ita zuwa dakin hutu. Uwale tace tana zaro manyan idanunta ke yar nan karki min rashin kunya, ya ina tambayarki me aka samu zaki min banza. Ki fada min gaskiya fari ne ko baki? Don wadan can yaran ko irin farin nan na jarirai wallahi baa haifesu dashi ba. Nurse ta kalli mal Yakubu tace masa namiji ne tayi gaba abinta.
Zulai kawar uwale ta kama hanci ta rangada guda. Uwale ta kuwa make ta, to uwar kinibibi ai baki ga kalar dan ba zaki cika mana kunne.
Batul Mamman
Title :
FARAR HAIHUWA💰 PART 1
Description : FARAR HAIHUWA 1 Bismillahir Rahmanir Rahim Kai kawo take tayi a siririn corridor din asibitin cikin tsananin tashin hankalin rashin ...
Rating :
5