A yayin da masoya, yan uwa da kuma masu sha’awar kallon fina-finan Hausa ke ta jimami na rashin fitaccen jarumin nan na barkwanci watau Rabilu Musa IBRO, kwatsam sai ga wani mai kama da shi ya bulla a masana’antar.
Arewa DailyPost ta samu labarin cewa yanzu haka dai matashin sabon jarumin Alasan Kanu ya samu damar fitowa a wani sabon fim mai suna ‘Jiki Magayi’ wanda a ciki kuma ya taka muhimmiyar rawa.
Idan ba’a manta ba dai Allah ya karbi ran marigayi Rabilu Musa Ibro ne kimanin fiye da shekara daya kenan bayan da yayi fama da gajeruwar rashin lafiya inda ba’samu wanda maye gurbin shi ba kusan sai a wannan lokaci.
Title :
Duniyar Fina Finan Hausa Ta Samu Magajin Ibiro.
Description : A yayin da masoya, yan uwa da kuma masu sha’awar kallon fina-finan Hausa ke ta jimami na rashin fitaccen jarumin nan na barkwanci watau Rab...
Rating :
5