...rashinsa babban rashi ne ga Nijeriya, cewarsa
Gwamnan jihar Bauchi, Barista Mohammed Abdullahi Abubakar ya bayyana rasuwar Danmasani Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule a matsayin babban rashi ga Nijeriya baki daya ba wai iya yankin Arewa kadai ba.
Yayin da yake yi wa shugaba Buhari, gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, iyalan mamacin da na daukacin al'ummar Nijeriya baki daya ta'aziyya, Gwamnan M.A Abubakar ya bayyana cewa ministan na Jamhuriyya ta daya, ya bar babbar gaba wanda zai yi wuya a cike.
A jawabin da aka rabawa manema labarai ta hannun sakataren yada labarai na jihar Bauchi, Malam Abubakar Al-Sadique, gwamnan ta bayyana Danmasanin Kano a matsayin daya daga cikin wadanda suka jajirce wajen samawa Nijeriya 'yanci, bada gudummawa wajen bunkasa Nijeriya kuma garkuwa ga matasa.
Title :
Danmasanin Kano Ya Rasu Yana Yi Wa Nijeriya Hidima, - Gwamnan Bauchi
Description : ...rashinsa babban rashi ne ga Nijeriya, cewarsa Gwamnan jihar Bauchi, Barista Mohammed Abdullahi Abubakar ya bayyana rasuwar Danmasani Ka...
Rating :
5