Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa ta sake kama tsohon Gwamnan Jigawa, Saminu Turaki saboda ya ki bayyana a kotu bisa zargin cin hanci da rashawa da ake yi masa.
An dai kama Saminu Turaki ne a Abuja a lokacin da ya halarci wajen kaddamar wani littafi kan tarihin hazikin Sojan Zakariya Maimalari wanda aka kashe a lokacin juyin mulkin shekarar 1966.
A shekarar 2011 ne, hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon Gwamnan a wata kotun tarayya da ke garin Dutse a jihar Jigawa bisa zargin karkatar da Naira Bilyan 36 daga asusun jihar.
Title :
Dalilin Sake Kama Tsohon Gwamnan Jigawa Saminu Turaki - EFCC
Description : Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa ta sake kama tsohon Gwamnan Jigawa, Saminu Turaki saboda ya ki bayyana a kotu bisa zargin cin hanci da ra...
Rating :
5