Babban hafsan rundunar sojojin Nijeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bai wa babban kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, wa'adin kwanaki 40 ya tabbatar ya kamo shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, a raye ko a mace.
Kakakin rundunar sojan Nijeriya, Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka shi ya sanar da haka cikin wani sako da ya aikawa kafafen watsa labarai, inda ya bayyana cewa an ba da wannan umarni ne a jiya Jumma'a, 21 ga watan Yuni, 2017.
Sanarwar ta kara da cewa, an bai wa babban kwamandan izinin ya yi amfani da duk wata dama da yake da ita don ganin ya gano inda Shekau yake tare da kamo shi.
Don haka ana bukatar jama'a su ba da hadin kai wajen ba da rahoton duk wasu bayanan sirri da za su kai a kama Shekau ko a ina yake a kasar nan.
Menene ra'ayin ku dangane da wannan umarni na shugaban sojojin Nijeriya? Wanne fata ku ke da shi na ganin Shekau ya shigo hannu?
Madogara: Zuma Times Hausa
Title :
Buratai Ya Ba Da Wa'adin Kwana 40 A Kamo Shekau A Raye Ko A Mace
Description : Babban hafsan rundunar sojojin Nijeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bai wa babban kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Manjo...
Rating :
5