Ministan Ilmi Adamu Adamu, ya bayyana cewa rikicin Boko Haram da ya sake tirnikewa a Maiduguri har ake yawan kai hare-hare a Jami’ar, ba zai sa Gwamnatin Tarayya ta rufe makarantar ba.
Adamu ya mika ta’aziyyyar sa ga jami’ar Maiduguri dangane da kisan gillar wasu malaman ta da Boko Haram su ka yi.
Ya ce gwamnati ba ta son a kawo cikas ga karatu a jami’ar, duk da hare-haren da Boko Haram su ka addabi jam’ar da Maiduguri su na kaiwa. Ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’a a ziyarar da ya kai jami’ar.
Sannan kuma ya jinjina musu kan irin tsayawar da suka yi su ka daure su na gudanar da ayyukan su duk da irin kalubalen matsalar tsaron da ake fuskanta.
“Kafin na zo nan, a da na yi tunanin rufe Jami’ar, amma bayan na saurari bayanin Mataimakin Shugaban Jami’ar.
Kuma na ga ayyukan da kun ke gudanarwa, to ina jinjina muku, kuma ina mai alfahari da ku matuka.” Haka Adamu ya bayyana.
“Don haka gwamnatin tarayya ba za ta rufe jami’ar ba, amma za ta taimaka da dukkan irin goyon bayan da ake bukata.
Sai ya nemi hukumar gudanarwar jami’ar da ta zauna ta tattauna yadda za a samar da ingantaccen tsaro a Jami’ar sannan ta gabatar wa gwamnatin tarayya da shawarwarin da su ka zartas.
Daga nan kuma ya kara yin ta’aziyya ga iyalan wadanda su ka rayukan su.
Tun da farko, Mataimakin Shugaban Jami’ar, Ibrahim Njodi, ya bayyana wa ministan cewa an kashe malaman jami’ar guda hudu, sai direban su shi ne cikon na biyar.
Title :
Ba za a rufe Jami’ar Maiduguri ba – Ministan Ilmi
Description : Ministan Ilmi Adamu Adamu, ya bayyana cewa rikicin Boko Haram da ya sake tirnikewa a Maiduguri har ake yawan kai hare-hare a Jami’ar, ba za...
Rating :
5