BA JARUMA MARYAM YAHAYA NAYI NIYYAR SAKAWA A SABON FIM DINA NA MANSOOR BA. inji Ali Nuhu
Babban Jarumin a masana'antar shirya fina-finan Hausa Jarumi Ali Nuhu yace ba Jaruma Maryam Yahaya yayi niyyar sakawa a sabon Fim din kamfanin shi mai suna Mansoor ba.
Sarki Ali Nuhu ya bayyana haka ga Jaridar Arewa Dailypost jim kadan bayan nuna sabon shirin a ranar biyu ga wata a babbar Silima dake Abuja.
Jarumin ya bayyana haka ne cikin kalubalen daya fuskanta a lokacin daukar sabon shirin mai suna Mansoor.
Yace lokacin da aka gama rubuta labarin har zuwa ranar farko da za'a fara daukar shirin ba Maryam Yahaya bace Jarumar, mun dauki lokaci mai tsawo muna jiran Jarumar da zata hau shirin amma bata zo ba shi yasa mukayi amfani da Maryam a matsayin gwaji kuma tayi daidai yadda ake so.
Ita Maryam da farko a cikin Shirin ta fito ne a daya yaga cikin Yaran makaranta amma ba babbar Jaruma ba; inji Ali Nuhu.
Arewa Daily Post
Title :
Ba Maryam Yahya Nayi Niyyar Sakawa A Sabon Fim Dina Na Mansoor Ba - Ali Nuhu
Description : BA JARUMA MARYAM YAHAYA NAYI NIYYAR SAKAWA A SABON FIM DINA NA MANSOOR BA. inji Ali Nuhu Babban Jarumin a masana'antar shirya fina-fina...
Rating :
5