An bai wa Gwamnatin Nijeriya wa’adin mako daya ta maidawa wakilin Sashen Hausa na tashar rediyon Deutsche Welle a Kaduna, Ibrahima Yakuba, kayan aikinsa da aka lalata, wata kungiyar kare 'yancin dan Adam da ake kira da cibiyar wanzar da zaman lafiya da adalci a Afirka, ita ce ta bayar da wannan waadi, tace bai kamata a rika cin zarafin 'yan jaridu ba.
Shugaban cibiyar, Dr. Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da kungiyar ta kira a Jos, ya ce 'yan jarida su ne ido da bakin talakawa, shi dai wakilin ya hadu da fushin 'yan sanda ne a Kaduna, yayin da ya ke daukar bayanai a wata zanga-zangar ranar Qudus ta 'yan Shi'a da ta so ta rikide ta zama arangama tsakaninsu da al'ummar gari.
Shi ma da ya ke bayani, shugaban kungiyar 'yan
jaridu reshen Jihar Filato, Yakubu Taddy, cewa ya yi akwai bukatar uwar kungiyar ta kasa ta sa bakinta cikin wannan batu, idan ba haka ba, wannan ma somin tabi ne kafin shekara ta 2019 a lokacin da kakar zabe da za a yi mai zuwa.
Sunday at 5:43am
Title :
An Zargi 'Yan Sanda Da Cin Zarafin Wakilin Tashar Rediyon DW Deutsche Welle A Kaduna
Description : An bai wa Gwamnatin Nijeriya wa’adin mako daya ta maidawa wakilin Sashen Hausa na tashar rediyon Deutsche Welle a Kaduna, Ibrahima Yakuba, k...
Rating :
5