Rundunar tsaro ta NSCDC reshen Nasarawa ta kama wani mutum bisa zargin harbawa wani yaro dan shekara 6 cutar sida (kanjamau) ta hanyar yi masa karin jini da jinin da ba'a tantance ba
Kwamnandan NSCDC, Lawan Bashir-Kano, ya shaidawa manema labarai a ranar Laraba a Lafia cewa mutumin dan kimanin shekara 30, Jonathan Ibrahim, ya bude asibitin da babu rajista yana likitancin bogi,
Mista Bashir-Kano yace a binciken farko likitan bogin ya tabbatar wa hukumomi cewa yakan durawa mutane mgunguna da jini ba tare da ya tabbatar da lafiyar jinanen ba, wanda garin haka ne ya durawa yaron jini mai dauke da kwayar sida (HIV)
Mista Bashir-Kano ya ce hukumarsu hadi da sauran hukumomin kiwon lafiya dake jihar zasu tabbatar an gurfanar da mutumin domin rashin hukunta ire-irensu shi ke kawo yawaitar likitocin bogi a kasar suna kashe mutane ba gaira-ba-dalili.
Ya kuma shawarci jama'a su yi taka tsanstan da irin asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da zasu rika zuwa ko kai 'yayansu. Sannan ya nemi jama'a dasu kai rahoton duk wani likita ko cibiyar kiwon lafiya da basu gamsu dashi ba.
Hausa times ta ruwaito wanda ake zargin yana shaidawa manema labarai cewa ya karanci muhalli da kiwon lafiya ne a jami'ar kimiyya da fasaha ta Keffi. Kuma ya tabbatar da cewa ya fara likitanci da bude asibitin duk ba tare da lasisi ba.
Me zaku CE? Me ya kamaci irin wadannan mutane?
Daga Hausa Times
Title :
An kama wani likitan bogi dake gogawa mararsa lafiya cutar Kanjamau a Nasarawa
Description : Rundunar tsaro ta NSCDC reshen Nasarawa ta kama wani mutum bisa zargin harbawa wani yaro dan shekara 6 cutar sida (kanjamau) ta hanyar yi ma...
Rating :
5