AN KADDAMAR DA DAN TAKARAR DAN MAJALISAR WAKILAI NA KWARE/WAMAKKO DOMIN CIKE GURBIN WANDA YA RASU A JIHAR SOKOTO
A jiya Larabar ne kwamitin yekuwar dan takarar dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Wamakko/Kware Hon Bello Haliru Guiwa ya kaddamar da fastar dan takarar a Ofishin Alhaji Muazu Zabira dake shiyar Gawon Nama a Birnin Sakkwato.
A wajen kaddamar da wannan fasta, 'yan siyasa daga Kananan hukumomin da zai wakilta da suka hada da Kware Wamakko masoya, 'yan Uwa da abokanin arziki duk sun samu halartar wurin.
Da yake yin tsokaci ga neman wannan kujerar ta dan majalisar wakilai ta tarayya wadda Allah ya yi wa mai wakiltar wadannan kananan hukumomi cikawa, Honarabul Bello Haliru Guiwa ya tabbatar wa al'umma cewa Ya fito Wannan Takarar ne sanadiyar kiraye-kirayen al'ummar wadannan kananan hukumomi.
Domin ya zo ya Wakilce su a majalisar wakilai ta tarayya, a sanadiyar rasuwar da mai Wakiltar su ya yi wa kwannin Baya.Hon Bello Haliru Guiwa Ya Bada tabbacin cewa, sanadiyar wadannan kiraye-kirayen ne, ya ga ya dace ya fito neman wannan kujerar domin samun ingantaccen wakilci ga al'ummar da suka nemi hakan.
A lokacin da yake yin tsokaci ga dan takarar Alhaji Muazu Zabira, ya bayyana kyawawan halayen dan takarar, inda ya bada tabbacin samun wakilci nagari, tare da da kawo ci gaba ga al'ummar da zai wakilta da ma jihar Sokoto baki daya.
Wadanda suka halarci taron sun hada da,
*Hon Shuaibu Gwanda Gobir.
*Abubakar Atiku, Tsohon S. A Na Speaker a Majalisar Wakilai ta Kasa.
*Alh Nasiru Tama
*Alh Sani Yar Abba, Da Sauran Masoya Da masu fatan alkairi.
Title :
AN KADDAMAR DA DAN TAKARAR DAN MAJALISAR WAKILAI NA KWARE/WAMAKKO DOMIN CIKE GURBIN WANDA YA RASU A JIHAR SOKOTO
Description : AN KADDAMAR DA DAN TAKARAR DAN MAJALISAR WAKILAI NA KWARE/WAMAKKO DOMIN CIKE GURBIN WANDA YA RASU A JIHAR SOKOTO A jiya Larabar ne kwamitin...
Rating :
5