Daga Jaridar Rariya
An shirya don shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki zai gana da Buhari a birnin Landan amma ya dawo ba tare da ya sami damar ganawa da shi ba.
Ana ganin wannan na da nasaba da yadda ake samun takun saka tsakanin majalisa da fadar gwamnati.
A ziyarar da ya ke a Ingila, ta bikin yaye dalibai a makarantar da dansa ke ciki, a karshen makon nan, an sa rai Shugaban majalisar zai gana da shugaba Buhari a Abuja House, inda ya ke jinya, sai dai hakan bai samu ba inda Bukola Sarakin ya dawo gida ba tare da ya sami ganinsa ba.
A cewar bayanai daga bangaren majalisar, an sa rai bayan ganawa da Faresa Yemi Osinbajo, za'a kuma bi kadin ganawar da shima shugaban majalisar sai dai ga shi hakan bai yiwu ba.
Takun saka ya karu tsakanin majalisa da gwamnati tun bayan tafiyar shugaba Buhari asibiti jinya, batu da ya kai wai har ana so a dora shugaban majalisar a matsayin shugaban kasa yayin da Farfesa Osinbajo ya yi bulaguro.
Batun tantance shugaban EFCC Magu, da ma batun daukaka kara zuwa kotu kan batun rashawa da cin hanci da gwamnati ta shigar kan shi shugaban majalisa duk dai ya kwaci6a al'amarin gudanar da mulki cikin raha tsakanin gwamnatocin masu cin gashin kansu a tarayya.
A yanzun da dawowar shugaba Buhari za ta nuna ko gaba ta kullu a tsakanin gaggan 'yan siyasar ne, ko kuma kawai rashin sa'ar ganin shugaban Bukola Sarakin ya yi.
Title :
An Hana Saraki Ganin Buhari A Birnin Landan
Description : Daga Jaridar Rariya An shirya don shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki zai gana da Buhari a birnin Landan amma ya dawo ba tare d...
Rating :
5