Mukaddashin shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya ba da umarnin karfafa tsaro a kudancin jihar Kaduna sakamakon rikicin da ya haddasa asarar rayuka da dama a ranar asabar da Lahadin da ta gabata.
A cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musammam ga mukaddashin shugaban kasar, Laolu Akande ya fitar, Farfesa Osinbajo ya jajanta wa dangin mutanen da rikicin ya shafa, kuma ya yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga mutanen da suka ji raunuka a rikicin.
Jami’an tsaro sun bayyanawa manema labarai cewa, zaman lafiya ya dawo kauyukan karamar hukumar Kajuru da ke jihar, inda rikici ya faru.
Daga Leadership
Title :
An Bukaci Karfafa Tsaro Kan Rikicin Kudancin Kaduna
Description : Mukaddashin shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya ba da umarnin karfafa tsaro a kudancin jihar Kaduna sakamakon rikicin da ya haddasa...
Rating :
5