Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cewa a Dajin Sambisa ya kamata a gina gidan kurkukun da za a rika garkame duk wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa.
Ya ce bin wannan mataki ya zama dole don nesanta barayin gwamnati daga cikin mutane yana mai cewa a halin yanzu akwai wasu manyan mutane da ke kokarin gurgunta ayyukan EFCC a kokarin da take yi na yaki da rashawa inda ya kuma kara jaddada muhimmancin hadin kan bangaren shari'a kan samun nasarar wannan yunkurin.
Rariya
Title :
A Dajin Sambisa Ya Dace A Gina Kurkuku Na Barayin Gwamnati - Magu
Description : Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cewa a Dajin Sambisa ya kamata a gina gidan kurkukun da za a rika garkame duk wanda aka samu ...
Rating :
5