Kwanaki kalilan bayan matasan Arewacin Najeriya sukayiwa yan kabilar Igbo barazana, kungiyar yan bindiga a Delta masu suna ‘New Delta Avengers’ya alanta fito na fito da gwamnatin Najeriya da kamfanonin man fetur da key akin.
Kungiyar ya bindigan ta lashi takobin cewa zasu cigaba da kai hare-haren Bam bututun mai da ke jihar Delta daga ranan 30 ga watan Yuni, 2017.
Kungiyar a wata jawabi ta bayyana cewa tana sanar da gwamnatin tarayya da kamfanonin mai su shiryawa durkusar da fitar da man fetur da iskar Gas.Kungiyar wada tayi ikirarin cewa gamayyar tsaffin yan bindiga ne ta bayyana ta kakakinta, CPL Oleum Bellum, cewa duk wanda yayi kokarin sulhu kuma zai dandana gudarsa.Sashen jawabin yace: “ Daga yankin fitar da mai a jihar Delta, mun hadu kuma mun yarje cewan zamu cigaba da kai hare-hare kafufuwan mai, zamu farfado da tsageranci kuma mu bukaci fansa mai kyau da kuma jihar mu ta Delta. Zamuyi wannan ta hare-hare masu zafi da kuma durusar da kamfanin man da ke jihar Delta.”
Title :
Zamu Cigaba Da Fasa Bututun Mai Daga Ranan 30 Ga Yuni – Kungiyar Tsagerun Delta
Description : Kwanaki kalilan bayan matasan Arewacin Najeriya sukayiwa yan kabilar Igbo barazana, kungiyar yan bindiga a Delta masu suna ‘New Delta Avenge...
Rating :
5