Fim ɗin Mansur, wanda fitaccen jarumin Kannywood Ali Nuhu ya shirya kuma ya bada umarni, labari ne na wani matashi ɗan gaba da fatiha.
Mahaifiyar Mansur ta yi ƙkokarin ɓoye masa wannan sirri game da asalinsa, sai dai soyayya ta sanya shi neman sanin gaskiyar al'amari.
Iyayen wata yarinyar da soyayya ta hada su a sakandare ne suka yi masa gorin asali, inda hakan ya tilasta masa katse karatu, ya bazama duniya don gano mahaifinsa.
An ƙkaddamar da fim ɗin Mansoor a jiya Alhamis ta hanyar nunin farko, a wani gawurtaccen biki cikin wata silima da ke birnin Kano, kuma sai a nan gaba ne za a fitar da faya-fayensa na bidiyo.
Sama da shekara goma da fara tunanin wannan fim, wanda aka shafe fiye da shekara biyu ana tsarawa da haɗa shi.
Daraktan fim ɗin, Ali Nuhu ya ce jigon Mansoor shi ne juriya da tawakkali don samun waraka ga wani halin alhini da ɗan'adam ka iya fuskanta a rayuwa.
"Akwai soyayya a cikinsa, amma jigonsa ba soyayya ba ce. Darasin da yake ƙkokarin isar wa al'umma shi ne duk abin da ka ga ya samu mutum a rayuwa...kar ka yi masa gori.
Kar ka tsangwame shi a kan wannan abu. Domin mai yiwuwa hanyar da Allah ya jarabce shi kenan, kamar yadda kai ma a matsayinka na ɗan'adam akwai hanyar da Allah ya jarabce ka."
Saɓanin yadda aka saba ganin fitattun jarumai a fina-finan Kannywood, a wannan karon an yi amfani da wasu sabbin fuskoki a matsayin manyan jarumai, da suka haɗar da Umar M Sharif da Maryam Yahaya.
Sama da shekara 20 kenan da fara harkar fina-finan Kannywood, amma masu sharhi na sukar cewa ba a sanya fasahar zamani sosai a cikin fina-finan ba.
Sai dai masu fim ɗin Mansoor sun ce sun yi ƙkokarin tunkarar wannan ƙkalubale wajen haɗa shi, don haka ne ma a cewarsu, fim ɗin ya kasance mafi tsada a duniyar Kannywood, don kuwa an kashe kusan naira miliyan takwas wajen hadawa da tallata shi.
Za a haska fim din a yau ne a sinimomin Shoprit, Kano, Genesis Deluxe Cinema, Ceddi Plaza, Abuja, Halimz Event Centre, Unguwar Rimi, Kaduna, Filmhouse Cinema Samonda da Filmhouse Cinema Dugbe, Ibadan.
Ga bidio talla fim din Mansoor
Title :
Yau Za A Haska Fim Din Mansoor A Sinimomi Daban-daban Dake Fadin Kasar Nan
Description : Fim ɗin Mansur, wanda fitaccen jarumin Kannywood Ali Nuhu ya shirya kuma ya bada umarni, labari ne na wani matashi ɗan gaba da fatiha. ...
Rating :
5