Rahotanni dake fitowa daga Kukau dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, na cewa an zo har gida an sake hakimin yankin tare da iyalinsa da yaransa an tsere dasun sai dai har yanzu ba'a san ko su waye ba, kuma basu turo sakon ko me suke so ba.
Da ga Hakimin Nathan Makama, mai shekaru 35, ya bayyana cewa, a ranar juma'a aka sace mahaifinsa da mahaifiyarsa da yaransu, kuma yace yaren hausa yaji suna yi da karin fillanci.
Ya kuma kara da cewa, dakaren da yayi kokarin kare mahaifin nasa ya rasa ransa a arangamar.A yankuna da yawa na jihar Kaduna dai, ana yawan samun matsalolin tsaro, da tashin-tashina tsakanin al'ummu dake zaune a jihar, kabilanci, addinanci da siyasa yana iya zama sanadiyyar yaki da barnar dukiyoyi tsakanin kabilu, shekara da shekaru.
Title :
Yan Bindiga Sun Sace Hakimi A Kaduna, Tare Da Iyalansa
Description : Rahotanni dake fitowa daga Kukau dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, na cewa an zo har gida an sake hakimin yankin tare da iyalinsa ...
Rating :
5