Rundunar sojin Najeriya ta bayyana kashe-kashen da aka yi wa Fulani a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin kasar a matsayin kisan-kare-dangi. Babban kwamandan runduna ta uku ta sojan kasar da ke Jos, wanda ya bayyana hakan, ya dora alhakin hakan kan shugabannin kabilar Mambila.
Birgediya Janar Benjamin Ahanotu ya fadi hakan ne a fadar Sarkin Mambila da ke jihar ta Taraba yayin wani taro da shugabannin al'ummomin yankin. A cewarsa, "An yanka kananan yara 'yan shekara biyu, an kashe mata masu ciki; abin da aka yi musu ya fi abin da 'yan Boko Haram ke yi, domin 'yan Boko Haram ba sa kashe kananan yara. Niyya aka yi ta yi musu kisan-kare-dangi".
Birgediya Janar Ahanotu ya kara da cewa, "Binciken da na yi ya yi yadda ake matukar nuna kiyayya ga Fulani a nan, sannan kuma an yi musu barna sosai; yanzu babu wani dan Fulani a wannan yanki in ban da wadanda suka gudu domin tsira, da kuma wadanda ke zaune a cikin gari. An yi yunkurin share su daga doron kasa ne."
Rariya
Title :
Yadda Aka Yi Wa Fulani Kisan Kiyashi A Taraba - Birgediya Janar Benjamin
Description : Rundunar sojin Najeriya ta bayyana kashe-kashen da aka yi wa Fulani a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin kasar a matsayin kisan-kare-da...
Rating :
5