Wani balarabe dan kasar Qatar mai shekaru 38 ya sanya ruwan gam din Super Glue, don toshe farjin matarsa, saboda zargin idan ya yi tafiya za ta iya aikata zina.
A dalilin wannan danyen hukunci da mijinta ya dauka a kanta, matar ta kai karar mijin nata gaban wata kotu dake birnin Doha.
Jaridar Doha Tribune ta rawaito cewa, mutumin ya tabbatar wa da kotu cewa, yana zargin matar tasa ne da nuna alamun sha'awar fasikanci, bayan da ya ga ta nuna goyon bayan (liking) 'posting' din da wani dan uwan sa ya yi a shafin sa na Facebook har sau biyu, sannan ya nunawa kotu wani hoton 'selfie' da matar ta dauki kanta, inda ake iya ganin takalmin da ta sa mai dunduniya.
Alkalin kotun Muhammad bn Sa'ad ya karbi uzurin wannan magidanci, bisa hujjar cewa bai yi hakan da nufin cutar wa ba. Ya kuma zargi matar da nuna halayen da ba su kamata ba, wadanda ke nuna alamun gayyata zuwa ga fasikanci.
Don haka an yanke mata hukuncin bulala 100, yayin da shi kuma mijin nata aka ci tarar sa Dala 10, saboda kuncin da ya haddasa mata a al'aurar ta.
Shin anya kuna ganin an yi adalci a wannan hukunci kuwa? Yaya ku ke ganin karfin zargin da wannan magidanci ya yi wa matarsa?
©Zuma Times Hausa
Title :
Wani Magidanci Ya Toshe Al'aurar Matarsa Da Super Glue' Don Zargin Za Ta Aikata Zina
Description : Wani balarabe dan kasar Qatar mai shekaru 38 ya sanya ruwan gam din Super Glue, don toshe farjin matarsa, saboda zargin idan ya yi tafiya z...
Rating :
5