A Zahirin gaskiya siyasa ana yin ta ne don riba, kuma duk Inda kaga jama'a sun zubawa Dan siyasa kuri'u to suna jiran su ga wani abu mai gauni na alheri ya same
su ne. Gudummawar da jama'ar Kano suka bayar wajen samun nasarar shugaba Buhari ba 'yar karama bace, domin Tun 2003
mutumin Kano ke zabar Buhari wandq hakan ta jefa jihar cikin ukubar siyasa daga hannun tsoffin shugabanni kamar Obasanjo da Ebele Jonathan. Duk da jajircewa ta Bakano wajen Nasarar Buhari
Yau jihar Kano da babbar kujera daya rak ta kare wato ministan cikin gida Inda jihar Bauchi tai Nasarar samun manyan kujera 7
a mulkin Buhari kamar haka:
Tabbas an baiwa 'yan Kano mukaman
"advisers" a wannan Gwamnati to irin
ruwan kuri'u da muka yiwa Buhari a 2015
mun fi karfin mu kare da masu basa
shawara da basa iya taimakon Kansu bare
su taimaki wani.
Naga ko Gwamnatin PDP da muka rika
adawa da ita kai har Jonathan mukaman
minista biyu ya bamu ga Shugabanin many
an hukumomin Gwamnati da muka samu,
to amma Yau a mulkin babanmu Buhari
mun kare da minista daya rak da 'yan
siyasa ke cewa bashi da masaniya a siyasa
da 'yan siyasar Kano.
Ga shi a baya abubuwan jimami iri iri sun
afkawa Kano amma duk da hakan Buhari
yaki kawo mana ziyara mu gan shi mu San
muma da gudunmawarmu a Nasarar da ya
samu, abubuwan da jama'a ke ta tambayar
shi ne anya bamu tura mota ta bude mu da
kura ba kuwa? Idan bamu amfana da
Gwamnatin Baba Buhari ba a Yau sai
yaushe ke nan? To ko mun yi wa Buhari
laifi ne? Idan laifi muka yi masa horon da
ake mana yayi yawa.
Comrade Bello Fagge.
09077742191.
Kwankwasiyya Reporters
KN/KR/0014
Title :
Wai mu 'Yan Kano me muka yiwa Buhari
ne?
Description : A Zahirin gaskiya siyasa ana yin ta ne don riba, kuma duk Inda kaga jama'a sun zubawa Dan siyasa kuri'u to suna jiran su ga wani ab...
Rating :
5