Rundunar sojojin Nijeriya ta ce ta yi nasarar kashe daukacin mayakan Boko Haram din da suka kai munanan hare-hare a wasu sassan birnin Maiduguri a daren jiya.
Daraktan yada labaran sojojin, Brigadier Janar Sani Usman Kukasheka, ya ce maharan sun kaddamar da harin ne a Yankin Jiddari Polo da ke cikin gari amma kuma sojojin sun samu galaba a kan su.
Sani Usman ya ce da farko mazauna yankin sun shirya tserewa daga gidajensu amma yanzu komai ya lafa.
Jami'in ya kuma tabbatar da karfafa tsaurara matakan tsaro tare da kara dakaru a yankin don hana barazanar irin wannan hari na bazata a na gaba.
Sai dai babu wani karin haske kan adadin wadanda suka mutu ko jikkata.
Harin na daren jiya ya kasance irinsa na farko da mayakan Boko Haram ke kai wa tun bayan karbe ikon wasu yankunan da ke karkashinsu.
Daga Rariya
Title :
Sojoji Sun Kashe 'Yan Boko Haram Din Da Suka Hari Garin Maiduguri A Aren Jiya
Description : Rundunar sojojin Nijeriya ta ce ta yi nasarar kashe daukacin mayakan Boko Haram din da suka kai munanan hare-hare a wasu sassan birnin Maid...
Rating :
5