- Wani dan kunar bakin wake ya yi kokarin tada bam a kusa da barikin soji na Giwa Barracks dake Maiduguri.
- Shugaban kungiyar ‘yan banga wato ‘Civilian-JTF’, Danbatta Bello ya fada wa majiyar mu cewa a ranar Talata da misalin karfe 2:40 na rana sojoji sun harbe wani dan kunar bakin waken a lokacin da ya ke kokarin shiga cikin bariki domin ya tada bam din.
“Mun kai gawan dan kunan bakin waken dakin ajiyan gawawwaki na wani asibiti a Maiduguri.”NAIJ.com ta samu labarin cewa Danbatta Bello ya ce hakan ya faru ne a daidai lokacin da wasu mazaunan sansanin Konduga ke jana’izan wasu ‘yan uwansu biyar da Boko Haram ta yi wa yankan rago a ranar Litini.Ya ce an gane cewa mutanen da Boko Haram ta yi wa yankan ragon mazaunan kauyen Balle Shuwari ne dake karamar hukumar Konduga.
Naij Hausa
Title :
Sojoji Sun Bindige Wani Dan Kunar Bakin Wake A Maiduguri
Description : - Wani dan kunar bakin wake ya yi kokarin tada bam a kusa da barikin soji na Giwa Barracks dake Maiduguri. - Shugaban kungiyar ‘yan banga w...
Rating :
5