Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya kori Sakatarensa Alh. Isa Sanusi Bayero saboda bayanan sirri da ya fitar daga fadar game da binciken sa da majalisar jihar tayi.
Isah Pilot kamar yadda aka fi kiransa shine sakataren tsohon sarki Marigayi Ado Bayero wanda bayan nada Sarki Sanusi sabon sarki sai ya ci gaba da amfani da shi a matsayin sakatarensa.
Gidan jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa har yanzu majalisar masarautar ba ta fitar da wani bayanai akan haka ba amma wata majiya ta sanar cewa sarkin ya riga ya nada Falakin Kano Alhaji Mustapha sabon sakataren sa.
Title :
Sarkin Kano Sanusi Ya Fatattaki Sakatarensa, Alh. Isa Sanusi Bayero.
Description : Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya kori Sakatarensa Alh. Isa Sanusi Bayero saboda bayanan sirri da ya fitar daga fadar game da binciken sa ...
Rating :
5