A Najeriya, a daidai irin wannan lokaci da yawanci abincin da mazauna karkara suka noma ya kai karshe, mutane musamman mata kan debo wasu ganyayyaki a daji da gonaki wadanda ake ci ta hanyar kwado da sauran hanyoyi na sarrafa ganyayyakin.
Yawancin mata tsofaffi da yara su ne sukan fita jeji ko bakin hanya domin ɗebo ganyen yaɗiya, sukan dafa ganyen tare da kwaɗwontawa don ci a matsayin abinci.
A wasu lokutan kuma sukan kasa domin kai wa kasuwa a sayar, a kuma sayo ƙarago ko ƙuli-ƙulin da za su yi kwaɗo a da shi.
Muhammad Annur Muhammad ya ga wasu mata da 'yan jikokinsu a yankin ƙaramar hukumar Kaugama ta jihar Jigawa suna ɗiban yaɗiyar.
Sun kuma shaida masa cewa tsanani ne yai tsanani a yanzu shi ya sa suma suka fito neman yaɗiyar, amma ba abu ne da suka saba yi ba.
Wata tsohuwa mai suna Mairo ta ce mutuwar mijinta ce ta sanya ala tilas ta ke fitowa neman abin da za ta ci, kuma yawancin ranaku naira ɗari kacal take samu idan ta ɗebo yaɗiyar ta dafa tare da kai wa kasuwa.
Wakilinmu ya rawaito cewa abin damuwar shi ne yara 'yan mata da ya kamata a ce suna makaranta a lokacin don ɗaukar karatu, su ke rako kakannin nasu ɗebo yaɗiyar.
Daya daga cikin su mai suna Adama ta shaida masa kullum suna rako kakanninsu don samun abin kai wa a baka.
Adama ta kara da cewa ''Kannenmu ne suke zuwa makarantar boko, mu kuma Islamiyya kadai muke zuwa, kuma ba wai cire mu aka yi daga makarantar ba, haka nan kawai muka daina zuwa''.
Hakan dai wani babban ƙalubale ne ga gwamnati, a daidai lokacin da ake faɗakar da iyaye sanin muhimmancin tura 'ya'yansu makaranta.
Batun matsin tattalin arziki dai na daya daga cikin matsalar da ke addabar 'yan Najeriya.
Har wa yau, tsadar kayan masarufi ta ƙara sanyawa masu ƙaramin ƙarfi shiga halin ni-'ya su ta fuskar cimaka da sauransu.
Title :
Rashin Abinci Ya Tilasta Wa Matan Karkara Cin Yaɗiya A Jigawa
Description : A Najeriya, a daidai irin wannan lokaci da yawanci abincin da mazauna karkara suka noma ya kai karshe, mutane musamman mata kan debo wasu...
Rating :
5