A yau ne Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi na biyu ya yi wannan hawa tare da tawagarsa. Tun bayan sallar La'asar ne Sarkin ya fito daga gida, inda Hakimai daga kananan hukumomi suka yi jerin gwano a kan titi zuwa Kofar Kudu.
Hakimin Wudil wato Makama shine farkon Hakimi, daga nan sai hakimai.
Sarkin dai ya je gidan mahaifiyarsa, wato Mai babban Daki dake Gwangwazo daga nan kuma ya fito ya sake hawa rakumi zuwa Kofar Kudu.
Manyan baki sun halarta kamar Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Ganduje, haka kuma baki daga kasashen duniya sun halarta.
Hakimin Karaye shine na karshe a tsarin hawan. An yi biki lafiya an kuma tashi lafiya.
Daga Rariya
Title :
Photos: An Yi Hawan Daushe A Kano
Description : A yau ne Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi na biyu ya yi wannan hawa tare da tawagarsa. Tun bayan sallar La'asar ne Sarkin ...
Rating :
5