Daga Rariya
Mukaddashin Shugaban Kasa, Osinbajo ya kai ziyara Maiduguri awowi bayan wani harin ba za ta da mayakan Boko Haram suka kai birnin.
Ya kai ziyarar ce don kaddamar ta fara wani gagarumin rabon kayan abinci ga 'yan gudun hijiran da rikicin Boko Haram ya shafa kimanin miliyan biyu a yankin arewa maso gabashin ƙasar. Wannan aiki, wanda jami'ai suka ce ba a taɓa yin irinsa ba, zai shafe tsawon kwanaki ana aiwatarwa, inda za a raba tan dubu talatin na kayan abinci iri daban-daban.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce harin da kungiyar Boko Haram ta kaddamar a garin Maiduguri dake jihar Borno a lokacin buda-baki ya kashe mutum 13. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Victor Osoku ya shedawa BBC cewa 'yan Boko Haram din sun kashe fararen hula 10, yayin da uku daga maharan suka mutu.
Title :
Photos: Osinbajo Ya Kai Ziyarar Maiduguri Awowi Bayan Harin Boko Haram
Description : Daga Rariya Mukaddashin Shugaban Kasa, Osinbajo ya kai ziyara Maiduguri awowi bayan wani harin ba za ta da mayakan Boko Haram suka kai birn...
Rating :
5