A safiyar yau Laraba ne kungiyar Jama'atul Izalatil Bidi'ah Wa Ikamatis Sunnah Reshen jihar Adamawa ta kaddamar da raba kayan tallafi ga marayu 2000 a jihar.
Alh Usman Ibrahim shine shugaban kwamitin marayun a jihar Adamawa kuma sakataren kwamitin a matakin kasa, a yayin da yake jawabi a wurin kaddamar da tallafin yace a wannan shekara an tantance marayu 2000 ne a wannan shekarar. Yace kamar yanda aka saba, kowani azumi kwamitin tasu ta marayu tana raba kayan tallafi makamancin wannan kowace shekara.
A yayin da yake jawabi, shugaban kungiyar Izala ta jihar Adamawa Alh Sahabo Magaji ya jinjina wa kwamitin na marayu, inda yace Taimakawa marayu na daya daga cikin manyan ayyukan kungiyar. Shugaba Sahabo yayi godiya ga jama'a bisa hadin kai da suka bada ta hanyar bada taimakon su.
Sheikh Dr. Abdulqadir Saleh Kazaure, malamin da kungiyar ta turo tafsiri a jihar Adamawa yayi jawabi ne akan falalan dake cikin tallafawa marayu. Shehin malamin yace falala dake ciki yana da yawa sosai, musamman idan akayi la'akari da hadisin da yace Manzon Allah zai yi tarayya da mai taimakawa maraya a gidan Aljannah.
©Mahmud Isa Yola
Jibwis Social Media Nigeria
26 Ramadaan 1438
21/06/2017.
Title :
Photos: Kungiyar Izala Ta Raba Kayan Tallafi Ga Marayu 2000 A Jihar Adamawa
Description : A safiyar yau Laraba ne kungiyar Jama'atul Izalatil Bidi'ah Wa Ikamatis Sunnah Reshen jihar Adamawa ta kaddamar da raba kayan talla...
Rating :
5