Marigayi Abdulhakim
Daga Jaridar Rariya
Rundunar 'yan sanda reshen jihar Bauchi ta samu nasarar kama karin wasu daga cikin wadanda ake zargi da kisan Abdulhakim Bauchin Bauchi.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar dauke da sanya hannun, DCP Chris Owolabi, tace ta kama mutanen cikin motar margayin kirar Mercedes Benz 300.
Rundunar tace an samu nasarar kama mutanen ne a sakamakon tsaurara matakan tsaro da aka yi a jihar a sakamakon bukukuwan sallah
Idan dai ba'a manta ba an yi wa margayi Abdulhakim Bauchin Bauchi kisan gilla ne a ranar 12 ga watan Maris 2017.
Allah ya jikan Abdulhakim
Title :
Photos: An Kama Wadanda Ake Zargi Da Kashe Abdulhakim Bauchin Bauchi
Description : Marigayi Abdulhakim Daga Jaridar Rariya Rundunar 'yan sanda reshen jihar Bauchi ta samu nasarar kama ka...
Rating :
5