Gwamnonin Nijeriya 36 Sun Gudanar Da Babban Taron Akan Karin Albashi Da Ma Wasu Matsalolin Jihohinsu
A daren Alhamis din da ta gabata ne Gwamnonin Jihohi 36 na Nijeriya suka yi zama na gaggawa a Birnin Tarayya Abuja karkashin Shugaban Kungiyar Gwamnonin kuma Gwamna Zamfara, Abdul-Azeez Yari.
A jawabin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Abdul-Azeez Yari, ya bayyana cewa sun tattauna ne akan abubuwa masu muhimmanci da suka shafi kada baki daya. Ya ce babban abinda suka fara magana akai shine lamarin da ya shafi ma'aikata na matsakaicin albashi, ya ce sun yanke shawarin barin kwamitin da Gwamnatin Tarayya ta nada su yi aikinsu.
Ya kara da cewa halin da Gwamnoni ke ciki a fili yake don har yanzu akwai Gwamnonin Jihohin da ba su biya albashin watanni ba, haka ya faru ne sakamakon yanayin tattalin arziki da suke fama da shi.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin yace a taron sun amince da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya biya kudin London Paris Club kaso na biyu, wanda za su yi amfani da kaso me tsoka wajen biyan albashin Ma'aikata da 'yan fensho.
A dalilin haka yace sun kafa kwamiti karkashin Gwamna Ondo me mambobi daga Jihar Bauchi, Sokoto, Plateau, Bayelsa, Rivers da tsohon Akawun babban bankin Tarayyar Najeriya(CBN) kuma Gwamna Gombe, hakan ya biyo bayan kararraki guda goma dake kan masu bada shawari ga Kungiyar Gwamnonin. Haka ne zai sa a gano matsalar masu bada shawari ga Kungiyar tun daga shekara ta 2005-2017.
A bangare guda kuma sun kalli lamarin bunkasa harkar siyasa. Kuma a zaman sun amince da su hada kai su ajiye bambancin siyasa don kyautata rayuwar al'ummar kasa baki daya. Hakan ya sa suka kafa kwamitin da zai daidaita lamuran Kungiyar tasu.
A jawabin sa ya kara da cewa muhimmancin su yasa babu wata magana da za'ayi ta siyasa ba'a ambace suba don kasancewar su ginshikai kuma masu amfani bisa irin gudumawar da suke badawa musamman a fanin cigaban siyasa.
Sannan yace kwamitin da suka nada me mutum bakwai ne karkashin Gwamna Jihar Imo me mambobi daga Jihohin Abia, Bauchi, Bayelsa, Ekiti, Kano da Nasarawa, wanda za su yi aiki ne akan habbaka cigaban siyasa da duba cikin al'amuran da suka shafi Kungiyar Gwamnonin don magana da murya daya.
Daga Rariya
Title :
Photos: Gwamnonin Nijeriya 36 Sun Gudanar Da Babban Taron
Description : Gwamnonin Nijeriya 36 Sun Gudanar Da Babban Taron Akan Karin Albashi Da Ma Wasu Matsalolin Jihohinsu A daren Alhamis din da ta gabata ne Gw...
Rating :
5