BAUTAR DA YA'YAN MUTANE DA SUNAN KARATUN AL-QURANI
Daga Sheriff Almuhajir
Daga garin Gombe, jiya wani aboki na kuma jam'in tsaro Ya kirawo ni a waya cikin bacin rai yana nuna mun halin da wani yaro Ya shiga da sunan Karatun Qurani.
Yaron sunan shi Hassan da bai wuce shekaru 6 ba, ya bayyana ma su cewa mahaifin shi ne ya kawo shi wannan gari domin Almajiranci, daga bisa ni baban ya rasu kuma bai san ina uwar shi ta yi aure ba. Ya kasance karkashin kulawar wannan Malami da ya ke azzaba shi kamar yadda kuke gani a cikin hoto.
A Yanzu dai malamin na hanun jamiah tsaro, ko da ya ke yace shi ma ajiyar yaron aka ba shi ba shine ainahin Malamin shi da ya sa a daure shi ba.
Al-ummar Arewa kenan; ana Jan hankalin su akan irin wannan zalumci da sunan Islama suna gardama, sai yaronnan ya shiga bh ya dauki bindiga yana karkashe su, sai su komo suna cewa Jonathan ne.
Allah Ya kyauta
Title :
Photos: Bautar Ya'yan Mutane Da Sunan Karatun Al-Qurani
Description : BAUTAR DA YA'YAN MUTANE DA SUNAN KARATUN AL-QURANI Daga Sheriff Almuhajir Daga garin Gombe, jiya wani aboki na kuma jam'in tsaro ...
Rating :
5