Sakamakon wa'adin da kungiyar matasan Arewa ta ba Igbo kan su fice daga yankin kafin ranar 1 ga watan Oktoba, Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo zai sadu da shugabannin Hausawa da Igbo da nufin sulhuntawa.
Haka nan kuma Mukaddashin Shugaban ya umarci jami'an tsaro kan su Karfafa Harkokin tsaro kafin cakar wannan wa'adin don ganin ba a samu wani hargitsi ba. A gobe ne dai za a yi zaman a Fadar Shugaban kasa.
Title :
Osibanjo Zai Gana Da Shugabannin Hausawa Da Igbo
Description : Sakamakon wa'adin da kungiyar matasan Arewa ta ba Igbo kan su fice daga yankin kafin ranar 1 ga watan Oktoba, Mukaddashin Shugaban Kasa...
Rating :
5