A Najeriya, wata ƙkasida da wani dan arewacin kasar ya rubuta kan mukaddashin shugaban kasa na tayar da kura a fagen siyasar kasar.
A cikin kasidar marubucin mai suna Dr. Ismaila Faruk daga jihar Zamfara, ya zargi Farfesa Yemi Osinbajo da nuna banbamci wajen nade naden mukamai.
Marubucin ya yi zargin cewa mukaddashin shugaban kasar na amfani da damar da ya samu wajen nada 'yan kabilarsa ta yarbawa da kuma mabiya majami'ar sa kan manyan mukamai.
Haka kuma murubucin ya ce hakan ya saba wa tanade tanaden kudin tsarin mulki.
Wasu masu sharhi a Najeriyar irin su Malam Bashir Baba, na ganin ba sabon abu ba ne ga masu rike da mukamai daga wasu shiyyoyi su rika aiwatar da muradun a'ummomin su sabanin yadda lamarin ya ke ga wasu masu rike da mukamai da suka fito daga arewacin kasar.
Sai dai ofishin mukaddashin shugaban ya yi fatali da wannan zargin.
Mataimakiya ta musamman kan harkokin shari'a ga mukaddashin shugaban Nigeria Dr Bilkisu Sa'idu ta shaida wa BBC cewa babu gaskiya a wannan zargi.
Ta ce ''akasarin manyan ma'aikatan dake tare da mukaddashin shugaban kasar 'yan arewa ne''- in ji ta.
Ta bada misali da wasu mukamai a ofishin mukaddashin shugaban kasar, inda ta ce masu wannan zargi kokari kawai suke yi su bata sunan mukaddashin shugaban kasa.
Title :
Osibanjo Na Nuna Kabilanci Wajen Nadin Mukamai, - Dr Ismail Faruk.
Description : A Najeriya, wata ƙkasida da wani dan arewacin kasar ya rubuta kan mukaddashin shugaban kasa na tayar da kura a fagen siyasar kasar. A ciki...
Rating :
5