Kimanin mutane uku ne suka rasa ransu a yau Litinin a Lokoja babban birnin jihar Kogi, yayin da 'yan bindiga suka bude wuta kan Sanata Dino Melaye.
Harin ya afku ne a gaban makarantar fasaha ta Kogi State Polytechnic, inda Sanata Melaye ya gabatar da jawabi ga magoya bayansa dangane da rikicin siyasar da ya bullo a mazabarsa.
A yanzu haka dai masu adawa da Sanata Dino Melaye su na cikin yunkurin yi masa kiranye daga majalisar dattawa bisa rashin amincewa da irin wakilcin da yake musu.
Ko yaya ku ke kallon wannan sabon rikicin kuma?
Title :
Mutane Uku Sun Mutu A Yayin Harin Da Aka Kai Wa Sanata Dino Melaye
Description : Kimanin mutane uku ne suka rasa ransu a yau Litinin a Lokoja babban birnin jihar Kogi, yayin da 'yan bindiga suka bude wuta kan Sanata ...
Rating :
5