A ranar Asabar, 3 ga watan Mayu, Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Hajiya Aisha Buhari ta kaddamar da cewa mijinta, shugaban kasa na samun sauki sosai.
Ta ba al’umma tabbacin cewa yana samun sauki sannan kuma zai dawo kasar nan ba da dadewa ba.
Aisha Buhari ta kasance babbar bakuwa a darasin Ramadan na 23 da kungiyar Ansar-ud-deen (ADS) ta gabatar a Abuja inda babban mataimakiyarta Dr Hajo Sani, ta wakilce ta.A cikin jawabin da Dr Sani ya saki a madadin Uwargidan shugaba Buhari, wacce ta tafi birnin Landan kimanin kwanaki 5 da suka wuce ta ce:
“Mijina na samun sauki sosai. Sannan kuma kwanan nan zai dawo kasar domin fara ayyukan sa.
“Ina godiya ga ‘yan Najeriya kan irin addu’o’in ga mijina. Don Allah kada ku gaza gurin addu’o’inku,” cewar ta.
Title :
Mijina Na Samu Sauki Sosai Kuma Zai Dawo Gida Sallah - A'isha Buhari
Description : A ranar Asabar, 3 ga watan Mayu, Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Hajiya Aisha Buhari ta kaddamar da cewa mijinta, shugaban kasa na samun ...
Rating :
5