amare da dama soyayyarsu tana mutuwa bayan aure tayanda kulawa ta kanyi karanci damuwa da juna ya ragu idan akayi la'akari da lokacinda ba'ayi aureba zakaga kusan kullum ana matse da juna marmarin kallon juna ake ba'ason rabuwa duk lokacinda aka hadu to amma abinda yafi bawa mutane mamaki shine lokacinda aka shaku kuma ya zama kullum ana tare sai kaga ana yiwa juna kallon raini musamman ango anfi samun raunin soyayya awajensa amma kuma manyan dalilai suna nuna laifin yafi fitowa daga wajen mace shiyasa naga tunda wannan darasi na amarene ya kamata amarya ta lura dasu domin karamin kuskure zai iya hanaki farin ciki tsawon rayuwarki
*WACCE IRIN SOYAYYA KUKAYI?*
soyayya da yan mata sukeyi akwai kuskure sosai acikinta ta yanda mace zata bawa namiji jikinta tamkar mijinta koda be sadu da itaba to zai zama kullum idan yaji sha'awa ita zata rika gamsar dashi wannan kuma ba karamin ruguza rayuwar aure yakeyiba duk wata soyayya da saurayi yake miki ko kuma Wanda kike masa kada Ki sake
Ko hannunki ya rike koda kuwa kin amincewarki zai kawo rabuwarku hakan shine zaisa kiyi mutunci tareda kima Wanda da dama wasu amare suka rasa awajen angwayensu amma koda wasa idan kika biyewa soyayya tareda bin son zuciyarki to tabbas ki shirya fuskantar wulakanci bayan aurenku
*KINJE DA BUDURCINKI?*
wasu amare tun daren farko ango yake fara daure mata fusaka saboda yajita sabani yanda yaji ana fada koda kuwa bashida ilimi akan jima i to zaiyi wahala ace besan menene budurciba
Abaya yana kallonki da kima yana ganin yayi sa'a to amma awannam Daren zai fara zarginki koda kuwa dashi kika bata budurcin naki zaiyi tsammani bashi kadai yayi mu'amala dakeba kuma koda kuskuren fahimta yayi to wannan zaisa yayita kallonki da abun matsala tayita girmama memakon abaya kuna mararin juna yanzu saikiga bayason zama kusa dake baya hira me dadi dake wani kuma shine musabbabin rabuwarsu shiyasa idan kinason kima to kada kiyi wasa da budurcinki sha'awa ta lokaci kadance daga kinyi hakuri zata wuce amma bakin cikin aure baya wucewa mummunan yanayine Wanda bazai bar zuciyarkiba saidai mutuwa ta rabaki dashi don haka mutuncinki a gidan miji tun kina budurwa zaki sameshi ta hanyar kyamar duk wata mu'amala da zata saka namiji taba jikinki
*RASHIN NUNAWA ANGO TAUSAYI*
Sauda dama zakaga ana soyayya sosai amma da zaran anzo hidimar biki sai kaga amarya tana matsawa ango yayi abinda bashi dashi haka zakaga ango yanata kashe kudi akan abinda ba farillah ba wannan baya batawa ango rai sai bayan biki domin wani bashin kudin zaiyi don ya faranta miki daga ransa ya bac dole zai rinka tuna abun yana ganinki amatsayin marar tausayi bashi kikesoba dan haka dole amarya sai kinyi hakuri kinbar abunda ba doleba don tausayawa angonki.
Title :
Ko Kinsan Meye Musabbabin Rugujewr Soyayyarku?
Description : amare da dama soyayyarsu tana mutuwa bayan aure tayanda kulawa ta kanyi karanci damuwa da juna ya ragu idan akayi la'akari da lok...
Rating :
5