Daga Mahmud Isa Yola
Biyo bayan kalaman da shahararren attajirin dan kasuwan nan Aliko Dangote yayi dangane da wa'adin watanni uku da kungiyar matasan arewa ta bawa kabilar Ibo na su bar yankin, kungiyar matasan tace batayi mamakin fitowan irin wadannan kalaman daga Dangoto ba.
Kungiyar a cikin wata takadda da ta samu rattaba hannun kakakin ta na kasa Abdul'aziz Suleiman tace abunda yasa Dangote ba zai goyi bayan wannan mataki nasu ba bai wuce muradun kasuwancin shi ba, amma ko kadan ba yana yi bane saboda Arewa.
Kungiyar tace abun takaici ne a ce Dangote ya fito yana sabawa matakin da ta dauka, wanda da dama daga cikin shugabannin Arewa na tare da shi ciki har da Farfesa Ango Abdullahi.
Kungiyar tace Dangote babu abunda yake tsinanawa yankin Arewa, saboda kashi 70 na kadarorin shi a kudu ya zuba su.
"Dangote da masu aniya irin tasa su san cewa matakin da muka dauka a Kaduna yana da muhimmanci da ba za su iya wanke shi da surkullen al'adun ba.
"Bama zaton Dangote zai amice da wani abu daga Arewa saboda ya riga ya fifita kudi akan 'yan uwan shi na Arewa, wanda hakan ne yasa Dangote, mafi dukiya a Afirika bashi da wani abun kirki da yayi a yankin da ya fito ko jihar sa ta Kano, yayin da kashi 70 na dukiyan shi ya zuba a kudu," inji kakakin majalisar a takaddan da ya fitar.
Har yanzu dai ana tafka muhawara akan matakin da matasan na Arewa suka dauka, inda wasu ke ganin dacewar hakan, wasu ko suna gani hakan bai dace da zaman lafiya ba.
Title :
Kai Ba Kowa Bane A Arewa, Martanin Kungiyar Matasan Arewa Ga Dangote
Description : Daga Mahmud Isa Yola Biyo bayan kalaman da shahararren attajirin dan kasuwan nan Aliko Dangote yayi dangane da wa'adin watanni uku da ...
Rating :
5