Hukumar Kwastan ta Kasa ta tara kudaden shiga har Naira bilyan 239.4 a farkon watanni uku na shekarar nan ta 2017. Wannan adadi ya fito ne daga Ma’aikatar Kudi ta Tarayya.
Wannan adadi na kunshe ne a cikin wasu takardun bayanan kudaden shigar da kwastan suka tara, wacce ta je hannun kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, NAN a ranar Litinin, a Abuja. Takardun bayanan dai su na dauke da dukkan bayan ayyukan da Ma’aikatar Kudi ta Tarayya ta gudanar a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Bayanan sun nuna cewa hukumar kwastan ta tara fiye da adadin da ta yi kintacen tarawa a cikin wadancan watanni uku na farko, inda ta yi kiyasin tara naira bilyan 193.2 a watanni ukun farkon wannan shekarar.
Ta ce hukumar ta samu wannan nasara ce ta hanyar gudanar da wasu muhimman sauye-sauye, gyare-gyare, yin wancakali da kawo abubuwan da ke kawo cikas ga tsarin tara haraji da kuma samar da hanyoyi masu saukin gudanar da ayyuka.
“A cikin 2015, Hukumar Kwastan ta Nijeriya ta tara harajin naira bilyan 904.07, sabani ko akasin naira bilyan 944.4 da aka yi kintacen tarawa a shekarar.
A 2016 kuma an tara naira bilyan 898.67 akasin naira bilyan 973.3 da aka yi kiyasin tarawa a shekarar wacce ta gabata.
” Tsakanin watan Janairu zuwa Maris na 2017 kuwa, Hukumar Kwastan ta tara haraji na kudi naira bilyan 239.4. Wato har ya haura kiyasin naira bilyan 193.22 da aka yi kintacen tarawa.” Haka takardar bayanan ta bayyana.
Har ila yau, hukumar ta bayyana ta na yin amfani da umarnin da fadar Shugaban Kasa ta bayar cewa idan kwastan sun kama duk wasu kayan da aka haramta shigo da su, to a gaggauta damka su ga a sansanonin ‘yan gudun hijira a Barno, Yobe, Adamawa da kuma sansanin Benin.
Title :
Hukumar Kwastan Ta Tara Naira Biliyan 239.4 A Farkon Watanni Ukun 2017
Description : Hukumar Kwastan ta Kasa ta tara kudaden shiga har Naira bilyan 239.4 a farkon watanni uku na shekarar nan ta 2017. Wannan adadi ya fito ne ...
Rating :
5