Wata tarzoma ta balle a garin Kontagora na jihar Naija wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane uku, ciki har da wani karamin yaro, yayin da wasu mutane 2, mace da namiji, suke jinya a yanzu haka.
Jaridar Rariya ta ruwaito wannan mummunan aika aika ya faru ne a ranar Alhamis 29 ga watan Yuni, kuma ya samo asali ne sakamakon rasuwar wani matashi da 'yan bangan garin Kontagora suka kama, suka lakada masa duka tun cikin watan Azumi.
Tun daga wannan lokaci ne fa matashin ya fara rashin lafiya, kuma mahukunta basu dauki hukunci akan 'yan bangan ba, har sai jiya da Allah ya yi ma wannan yaron rasuwa sakamakon jinyar da ya yi ta fama da ita, wanda wannan ne ya harzuka matasan garin, suka far wa ofishin 'yan bangan.
Rahotanni sun bayyana cewar an yi dauki ba dadi tsakanin matasan yankin da 'yan bangan, daga karshe dai matasan sun banka wa ofishin 'yan bangan wuta.
Title :
Hayaniya Ta Kaure Tsakanin Ýan Banga Da Matasa A Kontagora Har An Yi Kone Kone
Description : Wata tarzoma ta balle a garin Kontagora na jihar Naija wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane uku, ciki har da w...
Rating :
5